Masu sharhi kan harkokin siyasar kasar na cewa, bukatar kai ce kawai ta sanya jagororin bangarorin biyu takaddama da juna. A cewar masanin kimiyyar siyasa farfesa Kamilu Sani Fagge, manufar shugabannin biyu ba na su jagoranci jam’iyya bane, suna kokarin samun gindin zama ta siyasa domin ‘dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na zuwa ne daga Arewacin Najeriya.
Sai dai guda cikin dattawan jam’iyyar PDP kuma ‘dan kwamitin da ke kokarin sasanta Sanata Ahmed Makarfi da Sanata Modu Sheriff, Alhaji Sule Lamido, yace sun zauna da dukkan bangarorin tare da jin dukkan hujjojinsu, yanzu abin da ya rage shine samun hanyar da za a suhunta su, wanda hakan zai dauki lokaci.
Yanzu haka dai babban kotun tarayya a Port Harcourt ta umarci hukumar zabe ta INEC da hukumomin tsaro na DSS da Yan Sanda, su halarci babban taron na PDP gobe Laraba. Yayin da wata kotun tarayya a Abuja tace PDP ta dakata da yin wannan taro.
Saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano.