Wasu ‘yan bindiga sun kai hari akan jami’an tsaro a garin Inates na yankin Tilabery a iyakar Jamhuriyar Nijar da kasar Mali.
Harin wanda aka kai da yammaci jiya, na zuwa ne kwana daya bayan kai wani harin na daban da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji 3 a sansanin sojan Agando na Gundumar Tilia a yankin Tahoua.
Wadannan nan hare-hare, sun sake farfado da mahawara kan matakan da hukumomi ke dauka kan tsaron kasar ta Nijar.
Da misalin karfe 6 na yammacin jiya Talata ne wasu mutane akan babura dauke da bindigogi, wadansu kuma a motoci masu budadden kai wato Pick up, suka afkawa barikin sojan Inates na gundumar Ayorou yankin Tilabery a daidai lokacin da jami’an tsaro ke kokarin soma sallar magariba.
Majiyar wannan labari ta kara da cewa sojojin sun janye daga barikin a sakamakon lura da munin wannan al’amari da ke faruwa kwana daya tak bayan mutuwar sojoji 3,.
Hukumomi a gundumar ta Ayorou sun tabbatar da faruwar wannan al’amari ko da yake, ya zuwa yanzu, ana ci gaba da tattara bayanai don tantance barnar da abin ya haifar.
Amma wata majiya na cewa gumurzun da aka shafe sa’o’i ana yi ya haddasa asarar rayuka da dama a bangarorin biyu tare da kona motoci, da tarin kayan yaki.
A watan Yulin da ya gabata wani harin da aka kai a garin Inates ya hallaka sojojin Nijar kimanin 18.
Facebook Forum