Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Fada Ya Sake Barkewa A Birnin Aleppo


Mayakan 'yan tawaye na harba makamansu kan mayakan gwamnatin Syria
Mayakan 'yan tawaye na harba makamansu kan mayakan gwamnatin Syria

Wani sabon fada ya sake barkewa a jiya Lahadi a birnin Aleppo da sojoji suka kewaye, kwana uku bayan da aka dakatar da fadan don shiga da kayan agaji.

Wata kungiyar rajin kare hakkin bil adamata kasar Syria da mazauninta yake a Birtaniya ta “Syrian Observatory” ta ruwaito cewa sojan sama da na kasa sun koma ga kai farmaki akan garin.

Haka kuma Kungiyar ta Birtaniya tace an samu tashin rigingimun a wurare da dama a inda wannan tsohon birnin tarihi da aka raba shi tsakanin yammacinsa dake hannun gwamnati da kuma gefensa na yamma. Kungiyar tace Rasha da Syria duk sun sake komawa ga hare-haren da suke kaiwa.

Yanzu haka kungiyar ‘yantawayen ta ja kunnen mazauna garin na Aleppo da cewa su nisanci ma’aikatun gwamnati saboda hare-haren da ake jin za’a kaiwa ma’aikatun.

Wannan alma’arin ya tilastawa MDD dakatar da fidda marasa lafiya da tayi niyar yi a ranar Juma’a daga gabashin birnin Aleppo saboda rashin samun tabbacin tsaro daga bangarorin masu fada da junansu.

XS
SM
MD
LG