Hukumar kwastom ta kama mutanen ne bayan wasu bayanan sirri da suka samu, cewa akwai hauren giwa mai yawa da watakila ake shirin ketarawa da shi kasashen waje.
Batun ya dauki hankalin Majalisar dinkin duniya, da sauran kungiyoyin kare hakkin dabbobi, da wasu kasashe haramta fatauci, da kuma fasakwabrin hauren giwa da na wasu manyan namun dawa, da aka sayar dasu a kasashen ketare.
To sai dai kuma duk da matakan da ake dauka wasu 'yan sumoga, suna yin fasa-kwabrin zuwa kasashen ketare, inda dubun wasu ya cika akan iyakan jihar Adamawa da kasar kamaru.
Da yake nunawa manema labarai wasu kayayyaki da suka kama ciki, harda hauren giwaye, da kahunan bauna, Konturolan hukumar kwastam, mai kula da jihohin Adamawa, da Taraba, Kamardeen Olumoh,, yace sun sami nasarar cafke 'yan fasa-kwabrin ne, bayan wani samame da jami'ansu suka kai akan iyaka.
Banda hauren giwan, jami'an hukumar ta kwastam sun kuma samu nasarar cafke wasu kayayyaki da dama, ciki harda shinkafa, da man fetur, da ake kokarin fitarwa waje.
Wannan dai na zuwa ne yayin da yan kasuwa ke kira ga gwamnatin Najeriya da ta sake duba batun hana shigowa da wasu kayayyaki.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.
Facebook Forum