Kimanin jarirai miliyan biyu da dubu dari shida ke mutuwa a fadin duniya cikin wata guda da haihuwa, bisa ga cewar hukumar lafiya ta duniya. Galibin mace macen suna faruwa ne a kasashe masu tasowa inda ake fama da karancin cibiyoyin jinya. Cibiyar lafiya ta duniya dake birnin Housen tana kokarin shawo kan wannan matsalar ta hanyar wani shiri da ake kira NET360, wanda za a rika samar da muhimman kayayyakin aiki a asibitoci.
An zabi fasahar sarrafa kayan aiki iri goma sha bakwai da ake gani zasu taimaka wajen rage dalilan mutuwar jarirai, kamar ciwon hakarkari.
Kasashe kamar Malawi sun sami tallafin kayan aikin jinya a lokutan baya sai dai kwalliya bata biya kudin sabulu ba.
Daga cikin fasahun zamani goma sha bakwai da za a yi amfani da su, akwai wadanda za a iya saya a kasuwa yanzu haka, akwai kuma wadanda suke a matakin gwaji a halin yanzu, burin shine nan gaba, za a yi amfani da wannan fasaha wajen samar da kayan aiki, faro daga Mawali, daga nan kuma a samar da su ga dukan kasashen dake bukata.
Facebook Forum