Jam’iyyar MDC tana zargin hukumar zaben kasar da magudi a zaben da aka gudanar ranar talatin ga watan Yuli da nufin ba shugaba Emmerson Mnangagwa da jam’iyyarsu ta ZANU-PF galaba. Bisa ga sakamakon zaben da hukumar zaben ta fitar, Mnangagwa ya sami kashi hamsin da daya cikin dari na kuri’un, ya doke shugaban jam’iyar MDC Nelsom Chamisa, wanda ya sami kashi arba’in da hudu cikin dari.
Jam’iyyar MDC ta ce hukumar tayi arangizon kuri’un da ta ce shugaba Mnangagwa ya samu, ta kuma yi zargin cewa, kuri’un da aka ce an samu a wadansu mazabu sun fi mutanen da aka yiwa rajistar kada kuri’a yawa.
Chamisa ya shaidawa manema labarai ranar Litinin cewa, jama’iyarsa tana da shaida kwakkwara da ta nuna cewa an tafka magudi a zaben, ya kuma ce yana da kwarin guiwa kotu zata bada umarni a gudanar da sabon zabe.
Facebook Forum