Cikin watannin nan hudu na karshen shekara matsalolin tsaro na karuwa a kudancin kasar inda fashi da makami da satar mutane domin samun kudin fansa da kwace da karfin bindiga su kan neman zama ruwan dare gama gari a yankin.
Sabon kwamishanan 'yansandan jihar Edo Alhaji Haliru Gwandu ya bayyana ma'anar "Emba Months". Yace wadannan watannin sun fara ne daga watan Satumba zuwa Oktoba da Nuwamba da Disamba. Wadannan watanni ne da suka taso da bukukuwa daban daban. Baicin sallar Kirsimati lokaci ne da mutanen yankin ke samu suna zuwa garuruwansu daga sassan kasar da ma kasashen waje saboda haka sukan sa wasu bukukuwa ma daban daban har zuwa karshen shekara.
A wannan lokacin ne yara matasa da basu da dangana suke neman kudi ta hanyoyin da basu dace ba domin su ma su cimma muradunsu kamar kowa. Wasu su kan shiga yin fashi da makami. Wasu kuma su dinga satar mutane tare da aikata wasu abubuwa da dokar kasa bata amince dasu ba.
Inji Alhaji Gwandu babban sifetonsu Alhaji Ibrahim Idris ya basu oda kowa ya kai nashi shirin dakile laifuka a lokacin wadannan watannin.
Kwamishana Gwandu yace sun dauki duk matakan kare rayuka da dukiyoyin jama'a cikin wadannan watannin da al'ummar yankin suka camfa cewar watanni ne dake tattare da haddura daban daban.Duk kayan aikin da suke bukata walau na kasa ko na kan ruwa an tanadawa 'yansandan.
Kawo yanzu dai rundunar jihar ta kama bindigogi fiye da ishirin. Ta kuma cafke 'yan fashi da makami da masu satar mutane fiye da hamsin.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani.