Babban jami’in sojin Amurka yana zargin kasar Pakistan da goyon bayan kaiwa Amurka hare hare a Afghanistan.
Babban hafsan sojojin Amurka Mike Mullen ya shaidawa wani zaman majalisar dokokin Amurka cewa kungiyar Haqqani da ake alakantawa da al-qaida tare da goyon bayan cibiyar leken asirin kasar Pakistan ISI, ta kulla ta kuma kaiwa ofishin jakadancin Amurka hari makon jiya a Kabul.
Yace cibiyar leken asirin ta ISI ta kuma bada goyon baya a harin da mayakan Haqqani suka kaiwa wani sansanin kungiyar tsaro ta NATO a lardin Wardak dake tsakiya Afghanisatan ranar 10 ga wannan wata na Satumba wanda ya raunata sojojin Amurka 77.
Mullen ya bayyana cewa, cibiyar leken asirin ta kasar Pakistan tana amfani da kungiyar mayakan Haqqani wajen kaiwa Afghanistan da kuma dakarun hadin guiwa hari, ya kuma bayyana damuwa dangane da yadda ake kyale kungiyoyi masu tsatstsauran ra’ayi suna kai hare hare daga Pakistan.