Wani dan kunar bakin wake ya kashe tsohon shugaban kasar Afghanistan, kuma shugaban majalisar kawo zaman lafiya cikin kasar, Burhanuddin Rabbani, wadda yake jagorancin kokarin sulhu tsakanin gwamnati da ‘yan Taliban.
‘Yansanda suka ce maharin ya shiga gidan Mr. Rabbani jiya talata, ya tada bam da ya boye cikin rigarsa.
NATO sun aza laifin harin kan ‘yan kunar bakin wake biyu, wadan da suka fake da cewa sun je gidan ne da nufin gudanar da shawarwarin sulhu.
Akalla wasu mutane hudu sun mutu a fashewar, kuma daya daga cikin manyan masu baiwa shugaba Hameed Karzai shawara, Masoom Stanekzai, ya jikkata a harin.
Mr. Karzai ya gana da shugaba Obama a gefen taron majalisar dinkin Duniya, amma ya katse ziyararsa sabo da wan nan hari. A yau laraba da aka shirya zai yi jawabi ga babban zauren majalisar dinkin duniya.
Kamin su gana jiya talata, shugabannin biyu sun yi Allah wadai da kisan Mr. Rabbani. Shugaba Obama yace Burhanuddin mutum ne da yake da kishin Afghanistan. Shugaban na Amurka yace zai karfafa kudurin Amurka na ci gaba da aiki da Afghanistan domin cimma zaman lafiya.
Mr. Karzai yace tsohon shugaban kasan ya sadaukadda rayuwarsa domin Afghanistan da samawa kasar zaman lafiya.