Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye biyu a mintinan karshe a wasan da kasarsa ta Portugal ta buga da kasar Ireland a karawar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Kwallayensa sun sa an tashi a wasan da ci 2-1, nasarar da har ila yau ta ba shi dama ya kawar da tarihin tsohon dan wasan Iran Ali Daei da ya fi cin kwallaye ga kasarsa.
Ronaldo ya zura kwallon farko ne a minti na 89 yayin da Ireland take gaba a wasan da ci 1-0.
Kwallon ita ce ta 110 da ya ci wa kasarsa a wasanni 180 da ya bugawa Portugal.
Jim kadan bayan kwallonsa ta farko wacce ta kai wasan 1-1, Ronaldo ya kuma zura wata kwallon cikin mintinan da aka kara, abin da ya kai wasan 2-1 ya kuma ba Portugal nasara a karshe.
Sakamakon wasan ya ba Ronaldo dan shekara 36 damar wuce Daei wanda ya zura kwallaye 109 cikin wasanni 148 da ya bugawa kasars ta Iran.
Daei tsohon fitacce dan wasan kasar Iran ne da ya shahara a tsakanin shekarun 1993-2006 wanda mafi aksarin rayuwar kwallonsa ya yi ta ne a nahiyar Asiya.
Ko da yake, ya dan taka leda na dan kankanin lokaci a gasar Bundesliga ta kasar Jamus.
A farkon makon nan Ronaldo ya yi kome zuwa tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United bayan da ya baro Juventus a Italiya.