Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Robert Muller Ya Yi Magana Karon Farko A Bainin Jama'a


Robert Muller
Robert Muller

Mai bincike na musamman kan batun yin katsalandan da Rasha ta yi a zaben shugaban kasar Amurka na shekara ta dubu biyu da goma sha shida Robert Muller karon farko ya yi jawabi ga al'ummar Amurka ,ya kuma bayyana cewa, ba zai fadi wani abu da ya shige bayanin da ya yi ba dangane da batun

A jawabin farko da ya yi a bainin jama’a, tun bayan da aka nada shi mai bincike na musamman a shekarar 2017, Robert Muller, ya fada a jiya Laraba cewa binciken da ya gudanar bai nemi dorawa shugaban kasa laifin yiwa sashen shari’ar Amurka shisshigi ba, amma kuma hakan baya nufin shugaban bai aikata wani laifi ba.


Muller ya yi wadannan kalaman ne a ma’aikatar shari’a a Washington, inda ya bayyana batutuwan da dama da muhimmancin aikin binciken da aka bashi, domin tabbatar da yunkurin kasar Rasha na yin katsalanda a zaben shugaban kasar Amurka a shekarar 2016.

Yace kamar yanda yake kunshe a cikin wani zargin aikata laifi da rukunin masu taimakawa shari’a ya yi, wasu jami’an sashen leken asirin Rasha da suke tare da ma’aikatar sojin rashan sun kaiwa tsarin zaben Amurka hari. Zargin aikata laifin ya nuna sun yi amfani da fasahohin zamani masu karfi suka yi kutse a computoci da shafin yanar gizo da kwamitin yakin neman zaben Clinton ke amfani da su. Yace sun sace bayananta na sirri kana suka badda kamarni a kan yanar gizo da kuma shafin WikiLeaks suka kwarmata bayanan Clinton da suka sace.


Muller yace ya gudanar da aikinsa ne ta huskoki biyu, da farko ya gudanar da bincike a kan yunkurin yin katsalandan da Rasha ta yiwa zaben Amurka, kana ya kuma yi bincike a kan ko an yiwa binciken shisshigi, da ya hada da ayyukan shugaban Amurka Donald Trump.


Muller yace tsarin ma’aikatar shari’a ya nun aba za a iya dorawa shugaban kasa aikata laifi yayin da yake a karagar mulki, saboda haka ne Muller da ma’aikatarsa suka gaza dorawa shugaban kasar laifi.


A wani sakon Twitter a jiya Laraba, shugaba Trump yace Muller ya wanke shi daga aikata ba daidai ba, yana mai fadin cewa babu wani aikata laifi da rahoton Muller ya ayyana a kaina. Yace babu cikakken shaida a kan zargi da ake mini kuma a kasar mu mutum da babu shaida a kansa bashi da laifi. An rufe wannan Magana, Na gode, inji Trump.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG