Rahotanni daga jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa an rufe jami'ar gwamnatin tarayyar da ke garin Wukari, bayan zargin kashe wani malami da kuma wasu daliban jami'ar guda biyu.
A cikin 'yan kwanakin nan, an samu rahotannin bacewar wasu dalibai. Ana zargin cewa dalilin bacewar daliban yazo dab da tashe-tashen hankulan da ke wakana na rikicin kabilanci a tsakanin al'umma Tibi da na Jukun.
Wani dalibin jami'ar da tuni ya koma gida ya ce tun jiya suka soma fuskantar barazana inda ya bukaci hukumomi da a dau mataki don kare rayuka da ma'aikatan jami'ar, amma haka ya cutura.
Mahukuntan jami'ar ne suka fitar da wata sanarwar rufe jami'ar na har illa ma sha Allah, yayin da aka tura jami'an tsaro cikin al'amarin.
Kakakin rundunan 'yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal, ya tabbatar da rufe jami'ar, ko da yake, ya ce ba shi da cikakken bayani kan batun asarar rayuka da aka yi.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.
Facebook Forum