Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Siyasa a jihar Adamawa


Dakin Majalisar Jihar Adamawa
Dakin Majalisar Jihar Adamawa

A karon farko gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla, ya maida martani game da zaben tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a matsayin dan takarar babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP da cewa basa tsoron karo da maza.

Wannan kuma na zuwa ne yayin da jam’iyar APC a jihar Adamawa ke fama da rikicin cikin gida game da zaben fidda gwani.

Da alamun dai akwai ‘yan kallo a zaben shekarar 2019, ganin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku, shine yanzu dan takarar shugaban kasa, a inuwar babbar jam’iyar adawa ta PDP, yayin da ake ganin zai yi kokarin ganin ya samu nasara a jihar sa ta Adamawa, jihar da jam’iyar APC ke mulki a yanzu.

Ko a kwanaki, a wajen wani gangami a Yola, Atiku ya sha alwashin sai ya kawo jiharsa, inda ya ce sun san inda zasu kwance kurar da suka daure tun farko.

To wai ko anya cikin gwamnatin jihar bai dubi ruwa ba kuwa da zaman Atiku dan takarar PDP ayanzu? Kwamared Ahmad Sajo, dake zaman kwamishinan yada labaran jihar, ya ce ai su ko a gyalensu.

To sai dai kuma wannan na zuwa ne yayin da fusatattun yayan jam’iyar APC a jihar dake kokawa da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani na gwamna a jihar, ke cewa muddin uwar jam’iyyar bata soke zaben ba, to kuwa su shinkafa da wake zasu yi a zaben 2019.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG