Yakin neman zama dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar Republican da Rick Santorum ke yi ya sami gagarimin karfin gwiwa a jiya Talata bayan nasarar da ya yi a Minnesota da Missouri da kuma Colorado.
Bayan an tattara yawancin kuri’un, sakamakon ya nuna cewa tsohon dan Majalisar Dattawan Amurka daga Pennsylvania din yace muhimman kuri’un Minnesota da 45%, shi kuma dan Majalisar Wakilai Ron Paul ya zo na biyu da 27% , sai shi kuma tsohon gwamnan Massachusetts Mitt Romney, wanda aka dauka shi ne na gaba-gaba a ‘yan takarar Republcan, ya zo na uku kuma can baya ma da kuri’u 17%.
A zaben Missouri, bayan da aka kusa kammala kidaya, Satorum ya sami kashi 45%, Romney ya zo na biyu da 25%; sannan shi kuma Paul ya zo na uku da 12%.
A jawabin da ya biyo bayan nasarar da ya yi da yammacin jiya Talata a Missouri, Santorum ya yi shelar cewa “har yanzu akawi ra’ayin mazan jiya a Missouri da Minnesota muraran.”