Bisa ga dukan alamu mai neman jam’iyar Republican ta tsaida shi takarar shugaban kasar Mitt Romney yana kan hanyar samun gagarumar nasara a zaben share fage na jihar Nevada da za a gudanar yau asabar, bayan nasarar da ya samu a zaben share fage na jihar Florida.
Wani sabon binciken ra’ayoyin jama’a ya nuna tsohon gwamnan jihar Massachussetts yana kan gaba da babban abokin hamayyarshi tsohon kakakin majalisar wakilai Newt Gingrich da maki 20, inda Romney yake da kashi 45% Gingrich kuma yana da goyon baya kashi 25%. Binciken ra’ayoyin masu kada kuri’an ya nuna tsohon dan majalisar dattijai Rick Santorum na jihar Pennsylvania da kuma dan majalisa mai wakiltar jihar Texas Ron Paul suna baya.
Jihar Nevada tana daya daga cikin jihohi takwas da suke gudanar da zaben fidda dan takararsu kafin ranar shida ga watan Maris da jihohin goma suke zaben share fagensu, ranar da ake kira “Super Tuesday”.
Ana kyautata zaton Romney zai sami gagarumin goyon baya a jihar Nevada daga masu bin addinin Mormon. Ya lashe zabe a jihar lokacin da ya tsaya takara karon farko a shekara ta dubu biyu da takwas. Mabiya darikar Mormon ne kashi daya bisa hudu na wakilan jam’iyar Republican a jihar Nevada, yayinda kimanin kashi 95% daga cikinsu suke goyon bayan Romney.