Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya da hadin gwiwa da cibiyar bincike da bada horo kan harkokin demokaradiyya dake gidan Mambayya a birnin Kano sune suka shirya taron. Inda aka zabo malamai da shugabannin Majami’u kimanin 50 a ciki da wajen Kano, domin halartar taron wanda zai mayar da hankali akan rawar da jagororin addinan zasu taka wajen magance matsalolin rashawa da cin hanci tare da wanzar da shugabanci na gari.
Gabanin taron Mr. Shaaarik Zafar, ya gana da manema labarai don karin haske kan rawar da ofishinsa ke takawa wajen inganta hulda tsakanin Amurka da Musulman duniya kimanin Biliyan Guda da Miliyan Dari Shida, Zafar yace a matsayina na jakadan musamman aiki na shine tallafawa gwamnatin Amurka da ma’aikatar harkokin wajenta ta fuskar mua’mula ko hulda da musulman duniya.
Kafin ya bar jihar Kano Jakada Zafar, ana sa ran zai gana da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da maimartaba sarkin Kano Mallam Sunisi Lamido, haka kuma ya tattauna da kungiyoyin fararen hula kan muhimman batutuwan da suka shafi lardin na Arewa.
Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.