An shirya yin alluran rigakafin ne tun a lokacin da kasar ta fara samun mutumin da ya kamu da COVID-19 na farko.
Iyaye suna kin kai yaran su asibiti saboda tsoron za su iya kamuwa da kwayar cutar coronavirus da mutun dubu 17,000 suka kamu, kana ta yi sanadin mutuwar kusan dari 400.
Likitoci sun yi gargadin cewa idan ba tare da allurar rigakafi ba, yara a Kamaru suna cikin hadarin kamuwa da cuttukan da za a iya kaucewa kamuwa da su kamar cutukan bakon dauro da cutar makogoro mai hana nunfashi da kuma tetanus.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a wannan watan cewa, adadin yaran da ake yiwa allurar rigakafi na cuttukan da ake iya kare kai daga kamuwa dasu, ya yi kasa.
Facebook Forum