Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Ba Kananan Hukumomi Ikon Kasafta Kudinsu Ya Kawo Koma Baya


Mutanen kauye a zaune a bayan wata mota a lokacin da suke tserewa rigingimu a kusa da birnin Maiguduri.
Mutanen kauye a zaune a bayan wata mota a lokacin da suke tserewa rigingimu a kusa da birnin Maiguduri.

Rashin samun ‘yancin karbar kudaden kai tsaye daga asusun tarayya, na ci gaba da kasancewa babbar kalubala wajen tafiyar da harkokin mulki da shugabanci a matakin kananan hukumomi a Najeriya.

Batun ‘yanci ta fuskar kudade ga majalisun dokokin na jihohi da bangaren shari’a na jihohin da kuma kananan hukumomin Najeriya na cikin jerin abubuwan da majalisar dokoki ta Najeriya ta shigar sassan da aka yiwa kwaskwarima a cikin kundin tsarin mulkin kasar a kwanakin baya.

An sake tada wannan batu ne da nufin ganin ba kananan hukumomi ‘yancin samun kudadensu kai tsaye domin su iya gudanar da ayyuka ga al’ummominsu, bisa la’akari da cewa, wadansu kananan hukumomi sun zama kufai.

Masu kula da lamura na cewa, rike kudaden kananan hukumomi da aka yi shine ya haifar da talaucin da ake fama da shi a Najeriya da har yanzu aka kasa sanin hanyar fita daga ciki. Bisa ga cewarsu, kasancewa akwai dokoki da sharuddan amfani da kudaden, babu hujjar ba gwamnonin jihohi ikon kasafta kudadaden kananan hukumoni.

Bisa ga tsarin da ake bi yanzu dai, ya ana ba gwamnoni kudaden kananan hukumomi kafin daga baya su yanke hukumci kan yadda za a kasafta su.

Masu kula da lamuran sunce babu shakka majalisasun dokoki na jihohi suna da muhimmiyar rawar takawa wajen tabbatar da ‘yancin kudaden kanan hukumomi.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

'Yancin cin kashin kai a kananan hukumomi-3:34"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG