Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha da Turkiya Sun Tabbatar da Cigaban Dangantaka Tsakaninsu


Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Tayyip Erdogan

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan yana tababar ci gaba da danganataka tsakanin kasarsa da Rasha, bayan rahotanni da suka nuna sau da yawa jiragen yakin Rasha sun sha yin kutsawa cikin sararin samaniyar kasar akan iyakarta da Syria.

"Wasu matakai da bama son gani ana daukansu. Ba dai dai bane ga Turkiyya ta amince” dasu Inji Mr. Erdogan, a wani taro da manema labarai da tsakaninsa da Firayim Ministan Belgium a Brussels, kamar yadda jaridar Hariet ta kasar ta bayyana.

Turkiyya tayi sammacin jakadar Rasha a kasar a karo na biyu ranar Litinin bayan abunda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta kira "wani lamari da jiragen yakin Rasha suka sake kutsawa ta cikin sararin samaniyarta.

Mataimakin sakataren janar na Majalisar Dinkin Duniya Jens Stoltenberg ya fadawa manema labarai jiya Talata cewa, babu alamaun keta sararin samaniyar Turkiyya da Rasha tace tana yi ne bisa kuskure.

Wani mai fashin bakin Marcin Zabarowski ya gayawa sashen Farsi na Murya Amurka cewa Rasha tana son ta gwada iya hakurin kungiyar NATO ne ta wajen keta sararin samaniyar Turkiyya. Yace Rasha tana daukar wadannan matakai a dai dai lokacinda Turkiyya take kokarin kaucewa shiga rikicin dake akwai tsakanin Rasha da kasashe da suke yammacin duniya.

Daga bisani a jiya Talata, kakakin ma'aikatar tsaron Rasha Manjo Janar Igor Konashenkov, yace ma'aikatar tsaron Turkiyya ta bada shawarar kasashen biyu su kafa kwamitin tuntuba da zasu rika zantawa domin hana aukuwar lamura, a yayinda Rasha take daukar matakai kan 'yan kungiyar ISIS a hurumin Rasha.

XS
SM
MD
LG