Rasha da Iran suna kara kidima, ganin yadda ‘yan tawaye suke kara matsawa dakarun gwamnatin Syria lamba a kudanci da kuma gabashin kasar, da hari na baya bayan nan da suka kai a birnin Aleppo.
Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta bayyana jiya Talata cewa, jiragen saman yaki samfanin Tu-22M3 da Su-34 sun tashi daga sasanin mayakan saman Iran Hamedan domin kaiwa mayakan ISIS da kuma na alqaida hari da ake alakantawa da kungiyar Jabhat al Nusra a Aleppo da kuma Deir ex-Zor Idlib, bisa ga cewar ma’aikatar,
Duk da haka, sai kace hare haren da Rasha ke kaiwa, yunkuri ne na karawa dakarun dake tare da shugaban Syria Bashar al-Assad karfi.
Galibin tallafin yana zuwa ne ta kasa, inda ake ganin alamun kwararar mayakan da Iran ke marawa baya.