Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Mata Ta Duniya: Mata A Jihar Borno Na Neman Dauki


Wadansu 'yan gudun hijira da suka koma Guzamala.
Wadansu 'yan gudun hijira da suka koma Guzamala.

Matan da ke zaune a sansanan 'yan gudun hijira na cikin gida a jihar Borno sun bayyana takaicin ganin yadda su ke ci gaba da zama a takure shekaru bayan barin muhallansu sakamakon hare-haren Boko Haram.

Wannan rana dai ta samu mata da dama na wannan yankin a cikin mawuyacin hali musamman ma na rashin muhalli.

Daga cikin matan da Muryar Amurka ta yi hira da su a sansanan 'yan gudun hijira, akwai da dama da aka kashe mazajensu aka bar su da 'ya'ya marayu, wadanda su ke zaune da su a sansanan na tsawon shekaru.

Karin bayani akan: jihar Borno, Boko Haram, Nigeria, da Najeriya.

Da dama daga cikin su sun bayyana yanayin kunci da su ke rayuwa da ya hada da fargaban makomar 'ya'yansu kasancewa ba su samun sukunin makaranta kamar yadda su ka saba.

Wasu daga cikin mata ‘yan gudun hijira su nuna irin sana’o’in da suke yi kamar na dinkin hula da sauran su domin dogara da kai da ciyar da iyalensu.

A cikin hirar ta da Muryar Amurka, Hajiya Zuwaira Gambo kwamishanan harkokin mata ta jihar Borno ta yi karin haske akan wannan matsala da matan ke ciki da kuma abinda gwamnatin jihar ke yi.

Hajiya Zuwaira ta ce ana koyar da su sana’o’i domin su samu kula da iyalensu yayinda gwamnati ta dauke masu batun biyan kudin makaranta ganin yadda da dama su ke hana 'ya'yansu zuwa makaranta sabili da rashin kudin abincin rana da za su ba yaran.

Kwamishinar ta ce gwamnati tana tallafawa yaran da ke sansanin 'yan gudun hijiaran da kuma iyayensu mata domin su iya dogara ga kansu wata rana.

Ta kuma bayyana cewa, gwamati tana aiwatar da ilimin addini da na Boko Haram domin ganin cewa yaran sun tashi da cikakken ilimi.

Saurari rahoton Haruna Dauda Biu cikin sauti:

Ranar Mata Ta Duniya: Mata A Jihar Borno Na Neman Dauki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG