A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, mutane kimanin Miliyan 500 ne ke dauke da ita a fadin duniya, haka kuma mutane Miliyan ‘daya da rabi ke mutuwa a sakamakon cutar ta hanta a duk shekara.
Babbar illar da ke tattare da wannan cuta itace yadda akasarin mutanen dake dauke da cutar basu da masaniyar suna dauke da ita, duk kuwa da cewa masana kiwon lafiya sunyi amannar ta kan fi cutar HIV illa matuka, domin ita bata da maganin rage mata karfi da zarar ta kama mutum.
Dakta Aminu Idi, yayiwa wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin, karin haske kan wannan cuta, inda yace Hipatitis kala kala ce akwai wadda kwayoyin cutane suke shiga su yiwa hanta lahani, akwai kuma wadda zata iya yiwuwa guba ce mutum ya sha ta kuma yi masa lahani.
Bincike dai na nuna cewa mutane basu damu da gwajin wannan cuta ba har sai ta kai makura lamarin da likitoci suka ce yana da matukar hadari. Alamun cutar dai sun hada da ciwon kai a yawancin lokuta da amai da kasala da rashin cin abinci.
Saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin daga Lagos.