Wannan kuma ya biyo bayan umarnin da uwar jam’iyar ta kasa ta baiwa shugabanin jam’iyar a Adamawa ne na cewa su hanzarta karbar wasu tsoffin kusoshin jam’iyar irinsu Mallam Nuhu Ribadu,tsohon shugaban hukumar EFCC,batun da wasu kusoshin jam’iyar ke cewa ba zata sabu ba.
Hon.Ibrahim Hassan Bapetel wani hadimin shugaban Najeriya kan ayyuka da tsare tsare,yace ,ai jam’iyar ba gadon wani ba ce,da za’a hana wasu komowa. Kana yace,jam’iyar APC ,jam’iyace ta kowa wadda kofar ta a bude take don masu son komowa.
Shima wani jigon jam’iyar Mr Kube Wiberforce Donbulom,kuma tsohon shugaban karamar hukumar Guyuk,yace,’’kamata yayi a yabawa tsoffin shugabanin da suka kawo jam’iyar a jihar irinsu tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako,da kuma katukan Adamawa Mr Kobis Ari Thinmu.’’
Sakataren tsare tsare na jam’iyar a jihar Ahmad Lawal,yace su basu da wani bangare,inda yace wannan dambarwa bata rasa nasaba da irin hadakar da ta faru lokacin aka kafa jam’iyar a Najeriya.