A sakon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, yayi kira ga gwamnatoci da yan siyasa da yan kasuwa da kuma al’ummar kasa da kasa da su tashi tsaye wajen bayar da yanci tare da bada kariya ga kafofin yada labarai da ma’aikatan jarida.
Ban Ki-moon yace idan aka gaza ta wannan fuska to ko shakka babu an gaza wajen bayar da yancin da bil Adama ke da shi, wajen sanin abinda kan kai ya komo, ta haka ne kawai za a gudanar da aiki kafada da kafada domin ci gaban al’ummar duniya baki daya.
Shima a nasa bangarensa Farfesa Ralph Akinfeleye, shugaban sashen koyar aikin jarida na jami’ar Lagos, ya bayyana cewa ko shakka babu ya sabawa tsari irin na dimokaradiyya ya kuma sabawa al’adunmu na Afirka da aikin jarida ga duk wata gwamnati a duniya ta dauki matakan takurawa yan jaridu.
Ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai Mohammed, ya jaddada kudurin gwamnatin shugaba Mohammadu Buhari na ci gaba da bada hadin kai ga yan jaridu, tare da kare hakkokinsu domin gudanar da aiki bil hakki da gaskiya.