A arewacin jihar Adamawa, yankin da ya sha fama da rikicin Boko Haram, yanzu hankulan jama'ar wurin ya kwanta tunda shugaba Buhari ya kama mulki.
Jama'a na cigaba da yin harkokinsu cikin tsanaki ba tare da jin wani tsoro ba ko fargaban 'yan Boko Haram. Mazauna garuruwan sun ce fargaba ta ragu ainun saboda gwamnatin Muhammad Buhari.
Duk da cewa hankula sun kwanta akwai alamun wasu ba zasu taba manta abubuwan da suka faru ba.
Malam Danladi Muhammad, malami a kwalajin kimiya da fasaha ta jihar Adamawa yana cikin wadanda bam ya rutsa dasu a masallacin Juma'ar kwalajin. Yace har duniya ta nade ba zai manta da rikicin Boko Haram ba saboda ya rasa abokan aiki, da daliban da yake koyaswa da shi kansa domin ya jikata
Kwamishanan yada labarai na jihar Ahmed Sajo ya tuna yadda 'yan Boko Haram suka kwace garinsu na Mubi har suka sauya masa suna zuwa Birnin Musulunci. Yace yarsa ta bata a daji, tayi tattaki wajen kilomita 43 cikin dare a duhu.Iyayensa ma sun haura kan tsauni har suka isa Kamaru.Mahaifinsa da tsufansa sai da ya taka kusan kilimita 25 da kafa. Saboda haka yace shi ba zai taba mantawa da abun da 'yan Boko Haram suka yi ba.
'Yan Boko Haram ko jami'a basu barta ba. Sun shiga sun balle kofofi sun sace motocin makarantar da na asibiti.
Amma yanzu Allah da ikonsa ya maido da garin Mubi. Jama'ar garin sun rubanya wadanda suke ciki da saboda zaman lafiyan da aka samu.
Ga karin bayani.