Yanzu haka dai, tuni jama’a suka fara haramar azumin watan Ramadan, inda magidanta suka shiga kasuwanni domin sayayya. To ko yaya azumin na bana ya zo wa al’umma? ga ta bakin wasu a Jalingo da Yola wadanda suka ce sun shirya tsaf don shiga watan azumin.
A kullum akan zargi yan kasuwa da tsauwala farashin kayayyaki, musamman a wannan lokaci na azumi, batun da shugabanin yan kasuwa ke cewa ba laifinsu bane. Muhammad Ibrahim, shine shugaban kungiyar yan kasuwan Najeriya mai kula da jihohin arewa 19 yace ba haka lamarin yake ba.
Kawo yanzu ma tuni hukumomin tsaro suka fara daukan mataki na ganin an gudanar da azumin cikin tsanaki da kwanciyar hankali. SP Othman Abubakar kakakin rundunar yan sandan jihar Adamawa, ya bayyana matakin da aka dauka tare da yin kira ga kungiyoyin sakai na yan agaji.
Kamar wasu kasashe, ana sa ran fara azumin wannan shekara ranar alhamis.
Domin karin bayni saurari rahotan Ibrahim Abdul'aziz.
Facebook Forum