Duk da cewa Majalisar Dattawa ta ki amincewa da tabbatar da shugaban hukumar EFCC aikinsa, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa yana nan akan bakarsa na ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya har sai ranar da shugaba Buhari ya yanke shawarar matasayin da zai ‘dauka a kansa.
Wannan dai shine karo na biyu da shugaba Mohammadu Buhari ya tura sunan Ibrahim Magu, gaban Majalisar Dattawa don tabbatar masa da aikinsa. Shin me ‘yan Najeriya ke cewa game da wannna hukunci da ‘yan Majalisar su ka dauka?
Ya’u Chiroma Bakan Daura, yace kasancewar ‘yan Majalisa sun ki tabbatar da shi, Allah ne zai tabbatar da shi kuma a matsayinsu na ‘yan Najeriya suna nan suna yin addu’a kan duk wani da zai taimakawa shugaba Buhari a yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.
Shi kuma Mallam Salihu Isah Nataro, na ganin wannan aikin ‘yan Majalisa ne kamar yadda kundin tsarin mulki ya basu dama su yi binciken da suka yi, wanda sune suka san abin da suka samo akansa, saboda haka a amince abin da suka fada kasancewar ba Magu kadai ne a kasar ba zai iya wannan aiki.
Aliyu Alhazai Shinkafi, cewa ya yi magana ta gaskiya babu wani boye-boye duk abin da aka ga ‘yan siyasa sunki amincewa da wani abu da aka aiko daga fadar shugaban ‘kasa, to tabbas abu ne da bazai taimakesu ba ko amfanarsu.
Domin karin bayani.
Facebook Forum