Tambayoyin da suka yi ma Ibrahim Magu sun hada da ci gaba da rike Ibrahim Dasuki da kudaden da aka zargi tsohuwar ministar mai Deziani ta sata.
Sauran batutuwan sun hada da batun take hakkin dan Adam da na kudade da aka karba ya zuwa yanzu, sannan kuma da batun bin umurnin kotu.
Magu ya bayar da duk amsoshin tambayoyin da aka yi masa amma duk da haka majalisar ba ta gamsu ba.
A lokacin da ya ke bayyana dalilan da ya sa suka dauki wannan mataki, Sanata Kabiru Marafan Gusau, ya ce sun samu kansu rike da wasikar 'yan sandan farin kaya da ta yi bayani akan shi Ibrahim Magu.
A cikin wasikar ta ce Ibrahim Magu zai zamanto tamkar kayar baya ga gwamnati idan aka nada shi shugaban hukumar EFCC.
Wannan wasikar ta sake kawowa Majalisar rudani da rarrabuwar kawuna inda ra'ayoyi suka banbanta.
"Jam'iyyarmu ta APC bai kamata a ce ta ki bukatar shugaban kasa ba domin idan da akwai wata matsala kamata ya yi a warware ta kafin zamanmu na yau." In ji Sanata Mustapha Bukari.
A zamanta na yau ne kuma a karo na biyu, Majalisar Dattawan Najeriyar, ta sake kin amincewa da tabbatarwa da Magu mukamin shugaban hkumar ta EFCC.
"Ba za mu daina aikinmu ba fa...Ina kan bakana sai lokacin da aka ce in tashi. aikin jama'a mu ke yi kuma ba aikin ni kadai ba ne...Babu wanda zai ce shi kadai zai yi." In Magu a lokacin da ya gana da manema labarai.
Domin jin cikakken rahoto dangane da wannan lamari, saurari rahoton Medina Dauda.
Facebook Forum