Kasancewar zaben jahar Ondo ya ja hankulan mutune da dama, inda akayi ta kai ruwa rana kan wanda zai gaji gwamnan mai barin gado Olusegun Mimiko.
A cewar wani mazaunin jahar Mohammed Falalu, sunyi farin ciki sosai game da yadda zaben ya kaya, duk da cewar sun dade suna cikin wani hali game da harkar siyasa a jahar. Da kuma fatan sabuwar gwamnatin zata cika alkawuran da ta yi lokacin yakin neman zabe, sabanin yadda gwamnatin mai barin gado ta yi.
Ita kuma Aisha Bello, ta nuna jin dadin game da yadda aka gudanar da zaben ba tare da tashin hankali a jahar ba, haka kuma tayi kira ga sabon gwamnan da ya tashi tsaye wajen bunkasa kayyayakin more rayuwa da kasuwanci da taimakawa mata.
Shi kuma Anthony cewa bai ji dadin yadda zaben ya kasance ba, amma yayi kira ga sabon shugaban da tabbatar da adalci ga mutanen da suka zabe shi da ma daukacin mutanen jahar da zai mulka.
Domin karin bayani.