Dalilin da ya sa gwamnatin ta El-Rufai ta kafa kwamitin bincike na musamman a karkashin shugabancin Janar Marthin Luther Agwai tsohon hafsan hafsoshin sojojin Najeriya.
Kwamitin ya gano umalubaisan dalilin rikice-rikicen wadanda aka ce suna da alaka da zaben shekarar 2011. Rikicin zaben ya rutsa da wasu Fulani. An kashe wasunsu kana sun yi hasarar dukiyoyinsu. Shi ya sa wasu suka kwashe shanunsu suka koma kasashen da suka fito.
Kasashen sun hada da Kamaru da Nijar da Chadi da Mali da sauran kasashen dake makwaftaka da Najeriya. Irin wadannan Fulanin ne suke dawowa suna neman fansa.
Gwamnan yace sun samu mutane suna bi kasashen suna bada hakuri suna shaida masu an samu sabon gwamna a jihar Kaduna. Yace gwamnati ta fada cewa idan ta kama suna neman fansar kudi ne gwamnatinsa zata biyasu. Tun daga lokacin jihar ta samu lafiya.
To saidai kuma da wata matsala ta taso a Godogodo sarakunan wurin da Fulanin basu yi maza sun kashe wutar rigimar da ta taso ba har lamarin ya kaiga kashe kashe da kone konen gidaje.
Yace sun duba sun yi iyakar kokarinsu amma gaskiyar maganar ita ce akwai wasu tsirarun 'yan siyasa da suke ganin akwai anfani a tada hankalin jama'a. Su ne suke zuga mutane su ce wasu ba 'yan kasa ba ne bayan kuwa mutanen sun shekara dari biyu a wurin. Su kan ce ana kashe kabilun wurin ko kirista. Inji gwamnan duk irin wadannan maganganun ba zasu kawo zama lafiya ba.
Idan mutane suna karya doka a bar batun kabila ko addini a hukumtasu. Amma wasu suna anfani da lamarin suna son su kawo addini ko kabilanci ciki. Amma ita gwamnati tana ganin duk wanda ya aikata laifi a kamashi a hukumtashi.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.