Hukumar bunkasa sadarwa ta fasahar zamani ta Najeriya NITDA ta yi alwashin sada hanyoyin isar da sakonnin yanar gizo dukkan sassan kasar musamman yankunan karkara.
Shugaban hukumar sadarwar zamanin Dr.Isa Ali Pantami, ya baiyana haka bayan dawowa daga taron sadarwar zamani na duniya na bana da a ka gudanar a birnin Durban na Afurka ta kudu.Dr.Pantami ya ce akwai riba a lamarin sadarwar ta zamani in an debe kalubale da hakan ke tattare da shi ga al'ummar da wayewar ta isa gare su ba wadataccen wayar da kai.
Tsoffin jami'an gwamnati irin su Alh. Sanda izge sun yi na'am da wannan manufa musamman tasirin da za ta yi a jihohin da ke farfadowa daga illar Boko Haram.
Cibiyar bunkasa sadarwar yanar gizo CITAD ta gano cewa maza sun yi wa mata zarra a Najeriya wajen aiki da yanar gizo inda 10% na matan ke amfana yayin da na maza ya kai kashi 90%.
Saurari rahoton Nasiru Elhikaya...
Facebook Forum