Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Maharban Da Bom Ya Kashe A Maiduguri


An Jana'izar Manoma 43 Da Aka Yi Wa Yankan Rago a Borno
An Jana'izar Manoma 43 Da Aka Yi Wa Yankan Rago a Borno

An yi zana'iyar wasu maharba bakwai da suka gamu da ajalinsu yayin da su ka bi ta kan wani bomb da aka dana a kan hanya

Maharban sun gamu da ajalinsu ne a kyauyen kayamla dake karamar hukumar Jerry a jahar Borno, lokacin da su ke bin wasu da ake zaton 'yayan kungiyar Boko haram ne wandanda ake zaton sun sato wasu shanu.

Maharban sun bi ta kan wani bom da aka dana ne mai karfin gaske da ya tarwatse, ya yi sanadin kashe bakwai daga cikinsu yayinda wadansu tara suka ji mummunan rauni, wadanda suke jinya a asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri a halin yanzu.

Wasu Daga Cikin 'Yan Boko Haram Da Suka Sace 'Yan Matan Makarantar Chibok
Wasu Daga Cikin 'Yan Boko Haram Da Suka Sace 'Yan Matan Makarantar Chibok

Tunda farko dai sai da wadansu maharban su ka taka wani bom a kan yanyarsu zuwa Kayamla inda bom din ya fasa masu taya guda amma bai ji wa kowa rauni ba, suka kuma nemi taimako domin sake taya da ta lalace, maharban da suka gamu da ajalinsu sun kai masu dauki ne bayan sake tayar suna kan hanyarsu ta komawa, suka taka wani bom mai karfi da ya zama ajalinsu.

Wani maharbi da Muryar Amurka ta yi hira da shi, ya bayyana cewa, mutanen da suke kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun labe bayan dasa bom din da ya yi sanadin fashewar tayarsu suka jira wucewar motar da ta kai wa ta farko dauki kafin suka dana wani bom suka sake nokewa.

Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai Ya ziyarci Garin Gudumbali Dake Damasak
Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai Ya ziyarci Garin Gudumbali Dake Damasak

Kungiyar Boko Haram dai ta saba kai irin wadannan hare hare ta gudu ba tare da an kama wani daga cikinsu ba, lamarin da ke ci gaba da barazana ga komawa rayuwa ta yau da kullum a jihar.

Saurari cikakken rahoton da wakilinmu Haruna Dauda Bi’u ya aiko daga Maiduguri

An Yi Jana’izar Maharban Da Bom Ya Kashe A Maiduguri:3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG