Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Qatar Za Ta Fice Daga OPEC


Qatar ta ce za ta bar Kungiyar kasashe masu fitar da mai da ake kira OPEC a takaice daga watan Janairun shekarar 2019 domin maida hankali akan fitar da gas zuwa wasu kasashen.

A Yau Litinin, Ministan harkokin makamashi na Qatar Sa'ad Sherida Al-Kaabi ya bayyana wa manema labarai cewa kasar za ta fice daga Kungiyar OPEC.

Ya ce kasar da ta fi fidda gas waje a fadin duniya, tana shirin ta kara yawan gas din da take fitarwa daga tan miliyan 77 na zuwa tan miliyan 110.

Qatar kuma na so ta kara yawan man da take sarrafawa daga gangar mai miliyan 4.8 zuwa miliyan 6.5 duk rana.

Karamar kasar larabawar, mai arzikin makamashi na fuskantar takaddamar diplomasiyya da kasar Saudiyya, da ta mamaye kungiyar kasashen na OPEC.

Amma Al-Kaabi ya ce matakin fita daga kungiyar ta OPEC ba shi da nasaba da siyasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG