A baya dai mai baiwa tsohon shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa Ahmed Gulak, wanda bayan nasara a kotu ya ayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar.
A cewar Sanata Adamu Mu’azu, abinda ya dame su game da lamarin Gulak shine yunkurin juyin mulki da yayi da fara aiki gadan gadan. Ya kuma ce a baya ya hadu da Ahmed Gulak domi jin dalilinsa na yin hakan, inda ya bayyana masa cewa duk jam’iyyar PDP babu wani dattijo da ya kira shi yace abinda yake dai dai ne ko ba dai dai bane.
Ko ya PDP zasu kan kalubalen shugabannin jam’iyyar kamar su Bello Halliru da Olisa Metuh, dake fuskantar tuhumar almundahana, tambayar kenan da akayi Sanata Adam, wanda shi kuma yace har yanzu dai ba a gama bincike ba tukunna, tabbas ba za a iya yanke hukunci ba har sai kotu tayi. Duk da yake cewa baki dayansu sunce ba haka bane abinda ake tuhumar su.
Saurari cikakkiyar hirar.