Masana da kwararru a fannin kiwon lafiya da sauran masu ruwa da tsaki na kasashe daban daban na gudanar da taruka da laccocin fadakar da Jama’a dangane da matakan tallafawa masu da jama'a akan cutar farfadiya, a wani banagare na bukukuwan ranar cutar ta duniya.
Majalisar dinkin duniya ce daita ware kowace ranar litinin ta biyu a cikin watan Fabarairun kowace shekara domin gudanar da gangamin fadakarwa game da hanyoyin tallafawa rayuwar wadanda ke dauke da wannan cuta ta farfadiya.
A Kano cibiyar kula da masu wannan lallurar dake karkashe asibitin mkoyarwa na Malam Aminu Kano, ta gudanar da taron karawa juna sani, tsakanin jami’an kiwon lafiya, na asibitin da sauran kwararru.
Babban jami’in dake kula da cibiyar Dr. Aminu Taura, yace ita dai ciwon farfadiya ciwo ne da ya shafi kwakwalwa, duk abunda ya shafi kwakwalwa ya jawo mata wani rauni har tayi tabo, wannan tabon na iya zama tushen cutar farfadiya.
Matsalolin nan suna iya faruwa wani lokaci tun daga haihuwa irin yaran da ake samun wahala a lokacin da ake dauke da cikinsu da haihuwarsu su fito basu kuka, toh yakan faru wani lokaci idan sun taso sun samu farfadiya, wasu lokuta idan mutun ya kamu da ciwon sankarau bauyan ya warke bayan shekara daya ko bniyu sai a ganshi da ciwom farfadiya, har zazzabin Maleriya idan yayi zafi yana iya taba kwakwalwa duk abunda zai taba Kai, ko misali hadarin mota idan kai ya bugu anyi kwanaki ba’a san inda ake ba idan an farfado gaba sai ka ga ana sami ciwon farfadiya.