Masu zanga-zanga a wasu biranen kasar sun yi gangami a ranar Asabar don bayyana korafe-korafensu kan yadda gwamnatin APC mai mulki ke tafiyar da al’amuran kasar.
“Jam’iyyar PDP na Allah wadai da kakkausar murya, kan yadda sojojin haya na APC da Shugaba Muhammadu Buhari suka afkawa ‘yan Najeriya masu zanga-zangar lumana a ranar dimokradiyya.” Wata sanarwa dauke da sa hannun Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ta ce.
Najeriya ta yi bikin ranar Dimokradiyya 12 ga watan Yuni.
“Abin ya yi banbarakwai, a ce jam’iyyar APC da Shugaba Buhari, sun zabi su gallazawa ‘yan Najeriya ta hanyar amfani da makamai kamar yadda aka gani, duk da cewa, a lokacin da suka yi zanga-zangarsu a shekarar 2014 an bar su sun yi cikin kwanciyar hankali.”
Rahotanni da dama sun ruwaito cewa ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa masu zanga-zangar a biranen Abuja da Legas.
A cewar PDP, “ba abin mamaki ba ne, da shugaban ya kwashe sama da minti 20 yana jawabi (a jajiberin dimokradiyya) amma ya ki ya ambaci batun ‘yancin fadin albarkacin baki da yin taruka da kuma yin zanga-zangar lumana kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanada.”
Kokarin jin martanin jam’iyyar ta APC da hukumomin tsaro kan zargin na PDP bai yi nasara ba.