Yayin da Najeriya ke bikin ranar dimokradiyya, an gudanar da zanga-zanga a wasu sassan kasar inda matasa dauke da kwalaye da alluna, wadanda aka yi rubuce-rubuce a jinkinsu, suka mamaye wasu yankunan biranen kasar don bayyana korafe-korafensu.
A bara hukumomin Najeriyar suka mayar da ranar dimokradiyya zuwa 12 ga watan Yunin, sabanin 29 ga watan Mayu da aka saba yi, a wani mataki na girmama zaben June 12 da aka soke a shekarar 1993, wanda mutane da dama suka yi ittifakin shi ne zabe mafi sahihanci da kasar ta taba yi.
Mafi aksarin korafin masu zanga-zangar, sun ta’allaka ne kan yadda sha’anin tsaro ya tabarbare a Najeriyra, wacce ta fi yawan al’uma a nahiyar Afirka.
Baya ga haka, an ga da dama daga cikin matasan suna kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sauka mulki saboda abin da suka kira gazawar da gwamnatinsa ta APC ta nuna wajen tafiyar da al’amuran kasar yadda ya kamata.
A Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, rahotanni sun ce masu zanga zanga sun kai ruwa rana da jami’an tsaro, a lokacin da suka fara taruwa akan shataletalen Gudu, amma daga baya ‘yan sanda sun tarwatsa su ta hanyar amfani da hayaki mai sa kwalla.
Wasu allunan da masu zanga-zangar suka rike na dauke da sakonnin da ke cewa, “ ‘yancin fadin albarkacin baki, hakkinmu ne,” “A magance mana matsalar tsaro,” “Buhari ka sauka a mulki ka gaza” kamar yadda Channels ta ruwaito.
Babu wasu bayanai da suka nuna ko an jikkata a wannan zanga-zanga.
Rahotanni sun ce an wasu suna zanga-zangar kishi da masu sukar gwamnatin wadanda su me ke dauke da kwalaye na nuna goyon bayan hukumomin kasar.
Wakiliyarmu Shamsiyya Hamza Ibrahim, ta ruwaito cewa mafi aksarin tsakiyar birnin na Abuja ya kasance cikin yanayi na lumana domin an girke jami’an tsaro a sassansa.
A birnin Legas da ke kudu maso yammacin kasar, masu zanga-zangar sun taru ne a yankin Ojota, inda aka dasa wani mutumin M.K.O Abiola, wanda ake ikirarin shi ya lashe zaben na June 12.
Wakilinmu Babanbingda Jibril ya ce, ‘yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar daga baya gudun kada abin ya jirkice ya koma tarzoma. Sun yi amfani ne da hayaki mai sa kwalla.
Jama’a da dama sun kauracewa wuraren kasuwancinsu da fita yin harkokinsu na yau da kullum a birnin na Ikko, gudun abin da ka iya je ya zo.
A birnin Jos na jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya, al’amuran yau da kullum sun gudana yadda aka saba, ba tare da wata alama ta tashin hankali ba.
Sai dai an ga wasu masu zanga-zangar lumana da suka taru a Junction din Sakatariya dauke da kwalaye masu sakonni daban-daban.
“A inganta matakan tsaron Najeriya domin a kare mu,” “ba za mu taba sadaukar da ‘yancinmu na fadin albarkacin baki ba.” Wasu daga cikin sakonnin masu zanga-zangar lumanar suka nuna.
Wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji ta ruwaito cewa, an girke jami’an ‘yan sanda a yankin da masu zanga-zangar suka taru domin dakile duk wata tarzoma da ka iya tasowa.
Rahotanni na cewa a kudu maso gabashin Najeriyar, inda aka fi fargabar yiwuwar barkewra rikici, ba a samu wani tashin hankali ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Bayanai har ila yau sun yi nuni da cewa zangar zangar ta June 12, wacce masu fafutuka suka jima suna yekuwar a fito, ba ta yi tasiri a arewacin Najeriya ba.
Tun gabanin hakan kungiyoyi da dama a arewacin kasar, sun yi ta kira da a kaurcewa zanga-zangar.
A ranar Juma'a kungiyar daliban Najeriya ta NAN ta janye shiga zanga-zangar inda ta nesanta kanta da duk wata fafutuka ta nuna kin jinin gwamnati.
Bisa al'ada, bikin ranar dimokradiyya a Najeriya akan gudanar da shi ne da yin jawabai, taruka, faretin sojoji a biranen kasar, sabanin yadda ake gani a baya-bayan nan.
A jawabin da ya yi wa al’umar kasar a daren jajiberin ranar dimokradiyya, Shugaba Muhammadu Buhari ya fadi dalilin da ya sa gwamnatinsa ta sauya ranar Dimokradiyya daga 27 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni.
“Mun yi haka ne, don mu karrama saudakarwar da maza da mata suka yi ga kasarmu, wadanda suka yi fafutukar dawowar tsarin Dimokradiyya, mu kuma nuna yadda muka himmatu wajen ganin mun biya wa al’umarmu bukatunsu, ta yadda za a rungumi tsarin dimokradiyya a matsayin hanya madaidaiciya.”
Shugaban na Najeriya ya kara da cewa, “kamar kowane tsarin dimokradiyya, dole ne sai mun bi mataki daban-daban kafin dimokradiyyarmu ta kosa.”
Shugaban har ila yau, ya bayyana cewa, gwamnatinsa na daukan matakan kyautata rayuwar al’umar kasar musamman kan batun magance matsalolin tsaro.
“Tuni mun fara daukan matakan magance wannan matsala, kuma nan ba da jimawa ba za mu fara gurfanar da masu ta da zaune tsaye a gaban kuliya.”