Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Adamawa Alhaji Isa Shatima ya yi wannan furucin lokacin da Muryar Amurka ta nemi ta ji irin shiri da tanadi da hukumarsa ke yi domin zaben kananan hukumomi. Alhaji Isa Shatima ya ce hukumar na bukatar naira miliyan dari biyar domin gudanar da zaben.
Bincike da aka gudanar ya nuna jam’iyun siyasa goma sha takwas sun nuna aniyyarsu ta shiga zaben kananan hukumomin.
Alhaji Ahmed Lawal, sakataren tsare-tsare na APC ya ce tuni jam’iyar ta rufe sayar da takardun neman tsayawa takara wanda mutane 1,049 suka nuna aniyyarsu, daga cikin wannan adadin 145 mata da nakasassu ne.
Da yake magana kan shirin zaben kananan hukumomin shugaban jam’iyar SDP na jihar Mal. Ibrahim Bebetu ya gargadi ‘yan siyasa su yi farga cewa zaben bana ba zai yi kaman wanda ya kawo shugaba Buhari kan mulki ba, kowa zai yi ta kansa inji shi.
A daya bangaren kuwa jam’iyar PDP ce ke neman farfado da kimanta sakamakon takaddamar da ta yi sanadiyyar rusa zabe na jami’anta a mataki na kananan hukumomi da majalisar zartarwa ta PDP na kasa ta yi. Amma tsohon dan takarar gwamna kuma jigo a PDP Dr. Umar Ardo ya ce basu fargabar lamarin zai shafi farin jinin jam’iyar a idon masu zabe.
Ga karin bayani.