An kammala zagaye na uku a zabukan da aka shirya yi a Nigeria cikin wannan shekarar ta 2011.
Jiya Talata aka gudanar da zaben Gwamnoni da na ‘yan majalisar wakilan jihohin. An dai fuskanci tarzoma da tashe-tashen hankula a lokacin zabubbukan. Shaidun gani da ido sun ce mutane kalilan ne suka fita zuwa rumfunan zaben na jiya talata harma a wani yankin an sami rahoton hare-haren bom, a wasu sassan kuma babu isassun ma’aikatan zabe, yayin da a wasu wuraren ‘yan bindiga suka sace akwatunan zabe karfi da yaji.
Boma-bomai uku ne suka tashi a Maidugri dake yankin Arewa maso gabashin Nigeria. ‘Yan sanda suka ce babu wanda ya rasa ransa a hare-haren na jiya talata.
An fara bayyana sakamakon zaben wasu jihohin da suka hada da Legos inda Gwamna mai ci Fshoala na ACN ya sake lashe zaben, sai kuma jihar Kano da Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar PDP ya sami nasara. A jihar Nasarawa Gwamna mai ci Aliyu Akwai Doma ya sha kaye a hanun jam’iyyar hamayya ta CPC. A jihohin Borno da Yobe kuma ANPP mai mulkin jihohin ne ta sake lashe zabe.