‘Yan Najeriya sun jefa kuri’unsu a zabe na uku kuma na karshe da aka shirya a akasarin jihohin kasar. An dai fuskanci mummunar tarzoma da wasu tashe-tashen hankulan a lokacin zabubbukan. Shaidu sun ce mutane kalilan suka fito zabubbukan da aka yi jiya talata, inda a wani yankin aka fuskanci hare-haren bam, a wasu karancin ma’aikatan zabe, yayin da a wasu wuraren ‘yan bindiga suka sace akwatunan zabe karfi da yaji.
Bama-bamai uku sun tashi a Maiduguri dake yankin arewa maso gabashin Najeriya, kwanaki biyu bayan da wasu bama-baman suka kashe mutane 3 suka raunata 14 a wannan birni.'Yan sanda suka ce babu wanda ya mutu a hare-haren jiya talata. Daruruwan ma’aikatan zabe, wadanda akasarinsu ‘yan aikin bautar kasa ne, sun ki zuwa rumfunan zabe a arewacin kasar inda aka yi mummunar tarzomar ta makon jiya.
A yankin Niger Delta na kudancin Najeriya, ‘yan sanda sun ce sun samu bama-bamai biyu da ba su tashi ba, daya a kusa da wani ofishin hukumar zabe, dayan kuma kusa da wani ofishin gwamnati. Har ila yau a yankin na Niger Delta, ‘yan bindiga sun sace akwatunan zabe daga wasu rumfunan zaben.
‘Yan sanda sun kama wasu mutanen dangane da awun gaba da aka yi da akwatunan zaben. Gobe alhamis ne ake sa ran gudanar da zabubbukan gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da ma na tarayyar da aka dage a jihohin Bauchi da Kaduna, biyu daga cikin jihohin da aka fi fuskantar tarzoma a makon jiya.