A jiya alhamis aka yi zabubbukan gwamnoni a jahohin Najeriya biyu na Kaduna da Bauchi inda rikicin siyasa ya tilasta jinkirta yin zaben, inda kuma aka bada labarin cewa mutane ba su fita sosai ba.
Jam’iyyar shugaban kasa ta PDP ita ce ke rike da mulkin jahohin biyu amma a zaben na jiya alhamis sun fuskanci babban kalubale daga ‘yan takarar jam’iyyar CPC ta janar Muhammadu Buhari.
Zabubbukan gwamnonin da aka yi jiya alhamis su ne na ukku kuma na karshe a jerin zabubbukan da aka shirya yi a Najeriya a shekarar nan ta dubu biyu da goma sha daya. A zaben ‘yan majalisar dokokin da aka yi a farkon wannan wata, kujeru da dama sun kubucewa jam’iyyar PDP mai mulkin kasar.
Babban jami’in diflomasiyar Amurka mai kula da harakokin Afirka ya yabawa yadda aka tsara matakin da aka yi zabubbukan daki-daki a cikin wannan wata, Johnnie Carson ya ce wannan shi ne tsarin zabe mafi ingancin da aka taba gani a kasar Najeriya tun bayan mulkin soji a shekarar 1999. Karamin sakataren harakokin wajen Amurkar mai kula da al’amuran kasashen Afirka ya ce Amurka ta yi kaico da rikicin da ya barke a arewacin kasar bayan zaben shugaban kasar. Duk da haka dai Johnnie Carson ya ce amma a dunkule jami’an Amurka sun lura da yadda aka gaggauta daukan matakan tsaro sannan kuma sun yi fatan cewa wadannan zabubbukan na karshe, duk da dai ba su yi kyau kamar yadda ya kamata ba, su zama wani tushen kyautata zabubbuka a nan gaba.