Wani sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar PDP reshen Adamawa dangane da batun tsige gwamnan jihar Murtala Nayako da mataimakinsa Barrister Bala John Ngilari.
Kusoshin jam'iyyar sun goyi bayan a tsige gwamnan da mataimakinsa lamarin da ya raba kawunan 'ya'yan jam'iyyar a jihar.
Yayin da ya gana da manema labarai mataimakin gwamnan Barrister Bala John Ngilari ya zargi wasu 'yan siyasar jihar na PDP da cewa su ne suke neman a tsigesu domin suna neman hawa kujerar gwamna. Yace yayi mamaki da matakin da 'yan majalisa suka dauka yace gaskiyar maganar ita ce wasu dake zaune a Abuja ko a Yola ko a Madagali suke son aiwatar da aniyar domin cimma muradun kansu.
Amma daya daga cikin kusoshin jam'iyyar da suka halarci taron Dr. Umar Ardo yace ba haka zancen yake ba. Yace ba su ne suka yi ba. 'Yan majalisa suka yi kuma ba dole ba ne a gayyaceshi domin yana cikin zargi.
Wani malam Muhammed Yakubu mai nazarin harkokin siyasa yace akwai abun dubawa domin dambarwar tsige gwamnan da mataimakinsa. Yace an saba da yin haka a Adamawa. Haka siyasar Adamawa ta gada. Haka ma aka yiwa gwamnatin Boni Haruna lokacin da ta kusa kawo karshe. Haka ma gwamnatin tarayya ta shiga akai ta tukawa har gwamnatin ta kawo karshe.
Duk son kai ne ya jawo matsalar. Wasu na ganin idan basu yi hakan ba ba zasu samu komi ba kuma ga lokaci na kurewa. Irin wadannan mutanen suna neman karfafa matsayinsu ne kafin gwamnatin ta kawo karshe.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.