Gwamna Babangida Aliyu yana jawabi ne a zauren majalisar dokokin jihar a wani zama na musamman da majalisar ta shirya domin girmama marigayin Sanata Dahiru Awaisu Kuta a ranar Talatan nan.
Gwamnan ya karyata labarin da wasu ke yayatawa cewa akwai rashin jituwa tsakaninsa da marigayin. Gwamnan yace ko a Abuja ya fada cewa babu wata takaddama tsakainisu.
Shugaban majalisar dokokin jihar Adamu Usman ya bayyana dalilin gudanar da zaman musamman da majalisar tayi akan marigayin. Yace a shekarar 1983 marigayin shi ne mai ja kunnen 'yan adawar majalisar. Al'ada ce idan wani ya zama dan majalisa da can kana ya rasu akan girmamashi.
Shugaban kwamitin labarai na majalisar Bello Agwara yace akwai abun koyi ga matasan 'yan siyasa da marigayi Sanata Kuta ya bari. Ya bada gudummawa sosai ta nema wa matasa aiki da kuma kawo abubuwan moran rayuwa ga yankinsa.
Daruruwan jama'a da suka hada da iyalan marigayin suka cika majalisar dokokin domin sauraren zaman da majalisar ta shirya. Daga bisani an gudanar da addu'o'i har da na neman zaman lafiyar kasar.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.