WASHINGTON, DC —
Zaben gwamnan jihar Ekiti shi ne karo na farko da jam'iyyar PDP ta samu nasarar karbe kujerar gwamna daga babbar jam'iyyar adawa ta APC.
Jakadan Amurka a Najeriya yayi fatan zaben na Ekiti zai zama abun koyi ga zaben shekarar 2015, wato a yi zaben shekara mai zuwa cikin lumana kamar na Ekiti. Amma wannan zaben na Ekiti shi ya fi samun zuba ido daga hukumomin tsaro inda akalla 'yan sanda dubu talatin aka zuba a jihar.
Jam'iyyar PDP ta bukaci APC da ta rungumi kaddara dangane da sakamakon zaben. Ta kira APC ta tayata murna kamar yadda ita ma tayi lokacin da ta sha kaye a zaben gwamnan jihar Edo.
Tuni dai gwamnan Ekiti Dr Kayode Fayemi mai barin gado ya taya gwamna mai jiran gado Ayo Fayose murna inda yace idan zabensa shi ne zabin jihar Ekiti to ai shike nan.
Sai dai tambaya nan ita ce shin al'ummar Ekiti jam'iyya suka zaba ko dan takara. Wani masanin kimiyar siyasa Dr Sadiq Abba yace mutane da yawa sun gaji da yin adawa da gwamnatin tarayya domin basa ganin komi a kasa idan sun zabi 'yan adawa. Idan dai ba magudi aka yi ba to tunanin talakawa shi ne a tafi da gwamnatin tarayya domin su samu moriya kamar yadda suke gani a wasu jihohin.
Zaben jihar Ekitin ya nuna cewa babu wata jam'iyya da zata ce wata jiha tata ce kuma dole ta ci zabe a wurin. Komi na iya faruwa. A zaben 2015 tana yiwuwa jihohin dake karkashin PDP su koma APC, wadanda ke karkashin APC yanzu kuma su koma PDP. Idan za'a yi haka dimokradiya zata samu karfafawa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hkaya.