Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Papa Roma Francis Ya Soma Ziyarar Kwana Uku a Nan Amurka


Papa Roma Francis
Papa Roma Francis

Jiya Talata Papa Roma Francis ya iso nan Amurka a tashar jiragen sama na mayakan Amurka da ake kira Andrewas dake Jihar Maryland kusa da Washington DC.

Cikin wadanda suka tarbeshi harda shugaban Amurka Barack Obama, da uwargidansa Michele,da mataimakinsa Joe Biden da 'yayansu da kuma sauran manyan jami'an gwamnati dana cocin katholika.

Daruruwan mabiya darikarsa ne suke ta ambatonsa Pope Francis, Pope Francis da isowarsa. Daga nan jerin gwanon motoci suka dauki bakon zuwa masaukinsa inda gungun jama'a suka hallara suna masa marhabin lale anan Washington DC.Yaran makaranta da manya suna dauke da tutocin fadar Vatican,data Amurka data kasar Argentina kasar da Papa Roma ya fito.

Ya yada zangon farko anan Washington DC, a ziyarar da zata kaishi manyan birane uku da suke gabashin Amurka, sune Washington, da New York, da Philadelphia.

Papa Roma Francis yazo Amurka ne kai tsaye daga Cuba inda ya kai ziyarar aiki ta kwanaki hudu. Kasar da ya taka muhimmiyar rawa ta bayan fage na sake farfado da huldar difilomasiyya tsakaninta da Amurka.

Yau Laraba shugaba Obama zai karbi bakuncin Papa Roma a fadar White House.Shugabannin biyu sunyi haduwarsu ta farko ne a cikin watan Maris ta shekara 2014 a fadar Vatican.

An gayyaci Papa Roma Francis yayi jawabi a zaman hadin guiwa na Majalisun dokokin Amurka ranar Alhamis. Sannan zai yi jawabi ga babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a New York ranar Jumma'a. Ana sa ran Papa Roma Francis zai yi tattaki zuwa birnin Philadelphia inda za'a yi muhimmin taro domin iyali na duniya karkashin laimar majami'ar da yake yiwa shugabanci.

A jawaban da zai gabatar ana jin zai fi maida hankali ne da sukar tsarin jari hujja, da sukar lamirin manyan kasashen duniya kan tashe tashen hankula da suke mamaye duniya, da kuma kira kan batun bakin haure da 'yan gudun hijira da matsalar sakewar yanayi.

Ahalinda ake ciki kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ziyarar aiki a nan Amurka ta tsawon mako daya.

Mr. Xi yayi kira ga kan bukatar inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu domin ya taimaka wajen hana rikici barkewa tsakaninsu wanda aukuwar hakan inji Mr. Xi zai kasance mummunan bala'i tsakaninsu.

Mr. Xi ya furta hakan ne a birnin Seattle a jihar Washington a wani jawabi ga manyan 'yan kasuwar Amurka.

XS
SM
MD
LG