Papa Roma Francis ya yiwa dubban jama'a wa'azi a dandalin nan na juyin juya hali ko Revolutionary Square.
Yace kodayaushe ana kiran kiristoci su bar tasu manufar kamar neman iko ko mukami amma su mayarda hankalinsu akan wadanda basu da galifu. Yace Yesu ya bukaci kowane kirista ya kula da jama'a da kaunar juna ba tare da yin la'akari da abun da makwafci yake yi ba.
Daga bisani Papa Roman ya ziyarci tsohon shugaban kasar Fidel Castro a gidansa dake Havana tare da iyalansa suna kallonsu. Sun yi musayan litattafai da kyaututuka.
Daga nan kuma sai ya ziyarci shugaban kasan na yanzu kuma kanin tsohon shugaban Raul Castro. An kuma shiryawa Papa Roman ya gudanar da addu'ar yamma da wasu limaman cocinsa ya kuma yiwa matasa jawabi a zauren al'adun kasar.
Papa Roma Francis shi ne na uku da zai kai ziyara Cuba tun shekarar 1998 lokacin da Papa Roma John Paul II ya je tsibirin. A shekarar 2012 Papap Roma Benedict shi ma ya leka kasar.