Rahotanni daga kudu maso yammacin Najeriya na cewa wadanda suka yi garkuwa da tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Olu Falae sun nemi a biya miliyan 100 a matsayin kudin fansa.
Sakataren watsa labarai na jam'iyyar SDP, Remi Olayiwola, shi ne ya tabbatar da cewa anj nemi kudin fansar.
Bayanai na nuni da cewa an sace Falae mai shakeu 76 a gonarsa da ke Ilajo a Akure ta arewa a jahar Ondo.
Kakakin rundunar ‘yan sanda jahar ta Ondo Wole Ogodo, ya tabbatar da aukwar lamarin ga wata jarida da ake bugawa a kasar mai suna Daily Trust.
A rayuwarsa ta siyasa, Olu Falae ya taba rike mukamin shugaban jam’iyyar SDP, kana ya taba rike mukamin ministan kudi.
Tun bayan ritayarsa daga harkokin siyasa, Falae ya koma Akure, babban birnin Akure.
Ga karin bayani a wannan rahoto na wakilin Muryar Amurka Hassana Umaru Tambuwal: