Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyun Adawa Sun Hada Kai Don Kawar Da Gwamnan Jihar Bauchi


A jihar Bauchi jam’iyyun adawa guda biyar da kuma wasu daga cikin jam’iyyar APC mai mulki sun hade wuri guda domin kawar da gwamnan jihar Barrister Muhammed Abdullahi Abubakar daga kan kujera a zabe mai zuwa.

A ganawa da manema labarai da ya gudana a sakatariyar yan jarida wanda tsohon minista Alhaji Bello Kirfi ya jagoranta, yan takarar gwamna daga jam’iyyun sun amince kan bukatar a fitar da mutum guda domin su fafata da gwamna Muhammed Abdullahi Abubakar a zaben da za ayi.

Jam’iyun da su ka yi hadakar sune PDP da PRP da ADC da GPN da kuma PDM. A jawabinsa na bude taron ganawa da manema labaran jagoran hadakar jam’iyyun, Alhaji Bello Kirfi ya bayyana dalilan gudanar da hadakar domin a yaki gwamna Muhammed Abdullahi Abubakar.

Dakta Ali Pateh dan takarar gwamna a jam’iyar PRP ya jaddada goyon baya dangane da wannan bukata da ta haifar da kaddamar da hadakar jam’iyyun.

Dan takarar kujerar gwamna a jam’iyyar PDP a hadakar Sanata Bala Muhammed Kauran Bauchi, ya bayyana hadakar da cewa ita ce Bauchi.

Da ya ke fayyace matsayin gwamnatin jam’iyyar APC dangane da batun kirkirar hadakar jam’iyyun adawan, kwamishinan ma’iakatar yada labarai, al’adu da kuma yawan shakatawa Alhaji Umar Ibrahim Sade, ya ce wannan batu bai kawo musu sanyin gwiwa ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG