Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta shirya wani taron koli na kwanaki uku da ya hada da masu ruwa da tsaki daga ciki da wajen kasar don bitar cigaban da aka samu da kuma kalubalen da ake fuskanta wajen aikin yaki da cutar a kasar.
Wannan dai shi ne karon farko da aka shirya irin wannan taro tun bayan bullar cutar ta Covid-19 a Najeriya a watan Fabrairun shekarar 2020 lamarin da ya janyo koma baya ga harkokin rayuwa ta yau da kullum
Dakta Aminu Magashi Garba shi ne shugaban kwamitin da ya shirya taron, ya bayyana muhimmacinsa a wannan lokaci inda jami’ai daban-daban suka halarci taron don hadin kai wajen yanda za a yaki cutar a Najeriya baki daya.
Kawo yanzu dai mutane dubu 214, 513 ne suka kamu da cutar yayin da aka rasa mutane dubu 2980 daga ciki, mutane 207,403 sun kuma warke daga cutar dake rikida zuwa wasu nau’uka, Tsohon shugaban hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya Farfesa Abdulsalam Nasidi ya bayyana illar sabuwa nau’in cutar ta Omicron da ta bulla a kasar inda ya bayyana sabon nau’in akan abun tsoro saboda allurar rigakafi ma ba za ta iya hana kamuwa da cutar ba.
To sai dai a cewar shugaban kwamitin fadar shugaban kasa dake yaki da cutar ta covid 19 a Najeriya, Boss Mustapha kawo yanzu an samu nasarori amma muhimmin abu shi ne kara samun hadin kan jama’a wajen karbar allurar rigakafi
Taken taron dai shine kawo karshen Annobar ta Covid-19 tare da komawa rayuwar da aka saba ana kuma sa ran cimma hakan a shekara mai kamawa ta 2022.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: