Shugaba Barack Obama na Amurka da takwaransa China, Hu Jintao, sun jaddada muhimmancin hada kai – duk ko da yadda cewa lallai kam suna da sabanin ra’ayi game da kasuwanci da takardar kudin China da kuma batun ‘yancin dan adam.
Shugabannin kasashen biyu sun yi jawaban ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa a Fadar White House yau Laraba.
Mr. Obama y ace Amurka da China sun amince su cigaba da tattaunawa kan batun ‘yancin dan adam. Mr Hu ya amince cewa akwai sauran gyara sosai a China game da batun ‘yancin dan adam. Ya ce China na da niyyar ta shiga shawarwari da kuma musanye-musanye da Amurka a kan wannan batun cikin girma da arziki ba tare da yin katsalandan cikin harkokin cikin gidan juna ba.
Mr. Obama ya ce kasashen biyu za su iya cin gagarumar moriya idan sun hada kai. To amman y ace da bukatar China ta kara daukar matakan yin garanbawul ga darajar kudinta don ta daidaita kwarar da ke cikin huldar kasuwancin kasashen biyu.
Shugaban na Amurka ya ce sassan biyu sun cimma wasu yarjajjeniyoyi masu yawa da za su kara yawan abubuwan da Amurka za ta rinka sayar wa China da dala biliyan 45. Ya ce yarjajjeniyar ta kuma kara yawan jerin da China za ta saka da biliyoyin dala.